GWAMNA ZULUM YA KADDAMAR DA KE NUNA MASU AMFANI LANTARKI BAYAN HARAMTA AMFANI DASHI A JAHAR


By: Hamza Ali Usman

 Mazauna birnin Maiduguri da kewaye na cigaba da mafarkin bin sahun duniya a zamanance na cigaba amfani kekunan hawa masu amfani da lantarki bayan shafe watanni 13 da dakatar da Amfani da su da hukumomin jahar sukayi, A wani yunkuri na inganta harkar sufuri a jahar Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar ayyukan raya kasa da Gwamna Babagana Umara Zulum ya samar a tsakiyar watan Disamba mai karewa ciki har da keke napep, motocin taxi dama kekunan hawa masu amfani da lantarki.

Zulum project


   Wannan dai ba shine karon farko da gwamnatin jahar Borno ke samar abeben hawa ga al'ummar jahar a cikin farashi mai rangwame ba, wanda aƙalla akan samu sauƙin kaso hamsin cikin dari na farashin idan aka kwatanta da na masu zaman kansu.


   A cewar masu iya magana idan dambu yayi yawa baya jin mai, kasancewar birnin na Maiduguri da kewaye na ƙunshe da tarin al'umma hakan ya kara bukatar neman abin hawa daga lungu da sako na birnin musamman ga masu matsakaitan ƙarfi, duk da cewa masana tattalin arziki a Najeriya sun rushe wannan sashi na masu matsakaitan ƙarfi bisa dogaro da mizanin tattalin arzikin kasar, inda waɗannan rukuni suke cigaba nuna damuwa kan keke mai chaji, kwatsam sai gashi gwamna Babagana Umara Zulum ya gwangwaje jahar da motocin dake amfani da lantarki guda 100 da mashinan keke napep 500 motocin Bus Bus 42 hadi da kekuna 3000 dukkan su masu anfani da lantarki.


   Sai Dai ganin kekunan cikin jerin kayayyakin da aka ƙaddamar ya tayar da kura a cikin al'umma kasancewar an haramta amfani da shi a jahar tun a watan Nuwamban shekarar alif 2024 da ta gabata, inda jama'a ke daura kokonto kan ko an dage haramcin amfani da kekuna masu amfani lantarki ne, akan wannan batun na zanta da Mai magana da yawun gwamnan jahar Borno Mal. Dauda Iliya inda ya bani tabbacin cewa za'a sanar da al'ummar dukkan matakin da gwamnati dauka kafin raba kekunan ga wadanda aka tanada domin su, hakan nan ya ja hankalin jama'a tare da bayyana cewa kaddamar da kekunan baya nufin an dage dokar haramcin amfani da shi, inda ya bukaci a dakaci sanarwan hukumomi zuwa gaba. 

Comments

Popular posts from this blog

UKRAINE CITY THAT RUSSIAN ENVADED

Bikin Pizza day

Biggest Upgrade In History? Russia To Reactivate 800 Cold War-Era T-62 Tanks