Bikin Pizza day
A cikin makon nan ne akayi bikin Pizza Day a rant Litinin.
Shekaru goma sha uku (13 yrs) da suka wuce🔥, Menene Pizza Day.
Pizza Day rana ce da duniyar Crypto a cikin ta ake tunawa da wani mutum Engineer ne kuma Computer Programmer ne mai suna "Laszlo Hanyecz" dake zaune a jihar Florida ta kasar America, wanda a ranar 22 May 2010 ya saya wa iyalan sa Pizza guda biyu akan Bitcoin guda dubu goma (10,000 BTC) akan Dala 40 ($40 USD), ya bayar da Bitcoin dubu goma aka bashi Pizza guda biyu suka yi Breakfast.
~ A wancan lokacin kowane Bitcoin kwaya daya yana kan farashin Dala 0.004 wato ko Santi 'daya na Dala bai kai ba (less than One cent of Dollar).
~ A lissafin Dala a yau, a wancan lokacin mutumin ya sayi Bitcoin kwaya dubu Goma akan Dala 40, wato Kimanin Naira dubu 30,000 kenan. A yanzu idan kana son Sayan Bitcoin guda dubu goma sai kana da Naira Biliyan 'dari biyu da biyar (205 Biliyan Naira) domin kowane Bitcoin daya a yanzu yana kan Naira Miliyan 20,520,000 ne, a yanzu da Bitcoin ya ruguje kenan, Bitcoin yayi Araha ya fado 'kasa, ba kamar farashin sa na 2021 ba.
~ Mutumin ya bayar da Bitcoin dubu goma aka bashi Pizza guda biyu suka ci shi da 'ya'yan sa, a lokacin Dala 40 kenan, a yanzu kuma farashin Bitcoin guda dubu goma a Dalar Amurka shine Dala dubu 270,000 (205 Billion Naira).
Sayan Pizza da mutumin yayi da Bitcoin shine ciniki na farko da aka fara shi a duniya da Bitcoin (shugaban duk wani Crypto Coin a duniya), tun bayan da "Satoshi Nakamoto" ya kirki Bitcoin a 2007, aka yi Mining dinsa na shekaru biyu, zuwa cikin 2009 aka yi launching dinsa, a wancan lokacin duk Wanda yake da Computer 🖥️ duk bayan Mintoci 15 kana iya samun Bitcoin 5 ko 10, idan kana Mining dinsa.
Mutumin ya bayar da Bitcoin dubu goma ne a wancan lokacin saboda bai san cewa abun zai zo yayi daraja ya zama Digital assets ba nan gaba.
~ Shine yaci Abinci mafi tsada kenan a wannan zamanin namu na 22 century.
Comments
Post a Comment