GWAMNA ZULUM YA KADDAMAR DA KE NUNA MASU AMFANI LANTARKI BAYAN HARAMTA AMFANI DASHI A JAHAR
By: Hamza Ali Usman Mazauna birnin Maiduguri da kewaye na cigaba da mafarkin bin sahun duniya a zamanance na cigaba amfani kekunan hawa masu amfani da lantarki bayan shafe watanni 13 da dakatar da Amfani da su da hukumomin jahar sukayi, A wani yunkuri na inganta harkar sufuri a jahar Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar ayyukan raya kasa da Gwamna Babagana Umara Zulum ya samar a tsakiyar watan Disamba mai karewa ciki har da keke napep, motocin taxi dama kekunan hawa masu amfani da lantarki. Wannan dai ba shine karon farko da gwamnatin jahar Borno ke samar abeben hawa ga al'ummar jahar a cikin farashi mai rangwame ba, wanda aƙalla akan samu sauƙin kaso hamsin cikin dari na farashin idan aka kwatanta da na masu zaman kansu. A cewar masu iya magana idan dambu yayi yawa baya jin mai, kasancewar birnin na Maiduguri da kewaye na ƙunshe da tarin al'umma hakan ya kara bukatar neman abin hawa daga lungu da sako na birnin musamman ga masu matsakaitan ƙarfi, ...