Bikin Pizza day
A cikin makon nan ne akayi bikin Pizza Day a rant Litinin. Shekaru goma sha uku (13 yrs) da suka wuce🔥, Menene Pizza Day. Pizza Day rana ce da duniyar Crypto a cikin ta ake tunawa da wani mutum Engineer ne kuma Computer Programmer ne mai suna "Laszlo Hanyecz" dake zaune a jihar Florida ta kasar America, wanda a ranar 22 May 2010 ya saya wa iyalan sa Pizza guda biyu akan Bitcoin guda dubu goma (10,000 BTC) akan Dala 40 ($40 USD), ya bayar da Bitcoin dubu goma aka bashi Pizza guda biyu suka yi Breakfast. ~ A wancan lokacin kowane Bitcoin kwaya daya yana kan farashin Dala 0.004 wato ko Santi 'daya na Dala bai kai ba (less than One cent of Dollar). ~ A lissafin Dala a yau, a wancan lokacin mutumin ya sayi Bitcoin kwaya dubu Goma akan Dala 40, wato Kimanin Naira dubu 30,000 kenan. A yanzu idan kana son Sayan Bitcoin guda dubu goma sai kana da Naira Biliyan 'dari biyu da biyar (205 Biliyan Naira) domin kowane Bitcoin daya a yanzu yana kan Naira Miliyan 20,520,000 ne...